1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra’ila ta ƙaryata rahotannin cewa jiragen saman yakinta sun buɗe wa dakarun rundunar mayaƙan ruwan Jamus wuta a Lebanon.

October 26, 2006
https://p.dw.com/p/BueR
Dakarun kiyaye zaman lafiya na kasa da kasa a Afganistan
Dakarun kiyaye zaman lafiya na kasa da kasa a AfganistanHoto: picture-alliance/ dpa

Rahotanni daga yankin Gabas Ta Tsakiya sun ce jiragen saman yaƙin Isra’ila, sun buɗe wa sojojin rundunar mayaƙan ruwan Jamus, waɗanda ke girke a gaɓar Tekun Lebanon wuta. Jamus dai ta tura wasu jiragen ruwa da dakaru na rundunar mayaƙan ruwanta ne zuwa Lebanon ɗin, ƙarƙashin laimar dakarun kare zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya, sakamakon yarjejeniyar da aka cim ma don kawo ƙarshen yaƙin da Isra’ilan ta gwabza da ƙungiyar Hizbullahi a Lebanon.

Ma’aikatar tsaron Isra’ilan dai tuni ta ƙaryata wannan zargin.

Game da wannan batun dai, ministan tsaron Jamus Franz Josef Jung ya ce ya yi fira a kan wayar tarho da takwaran aikinsa na Isra’ila Amir Perez, wanda ya tabbatar masa cewa rahotannin ba su da wani tushe. Da yake amsa tambayoyin maneman labarai a wata fira da ya yi da gidan talabijin nan ZDF na nan Jamus, Franz Josef Jung ya bayyana cewa:-

„Ɗazu ɗazun nan na tattauna a kan waya da takwaran aiki na na Isra’ila wanda ya nanata mini cewa babu wani jirginsa da ya buɗe wa dakarunmu wuta, babu kuma wani abin da ya auku a yankin. Kazalika kuma ya tabbatar mini cewa ƙasarsa na ɗaukar wanzuwar dakarunmu a yankin da muhimmanci, saboda namijin ƙoƙarin da muke yi wajen ganin cewa an tabbatad da zaman lafiya a Lebanon.“