1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ta kai hari a Gaza

September 5, 2010

Isra'ila ta ƙaddamar da harin da yayi sanadiyyar mutuwar mutum guda a zirin Gaza

https://p.dw.com/p/P4oQ
Hoto: AP

A safiyar yau Lahadin nan ne jiragen yaƙin Isra'ila suka kai wasu jerin hare-hare har guda uku a yankin zirin Gaza. Biyu daga cikin hare-haren dai an kai sune kan hanyoyin ƙarƙashin ƙasar nan da suka haɗe yankin na Falasɗinawa da ƙasar Masar.

A cewar wasu majiyoyin Falasɗinawa aƙalla mutum guda ne ya rasa ransa, kana wasu uku suka samu raunuka. Inda shi kuma hari na uku aka kai shi kan tsohon sansanin dakarun Hamas dake Yunis. To amma dakarun sojin Isra'ila sun bayyana waɗannan hare-hare da cewa na ramuwar gayya ne bisa harin roka da aka harba musu daga yankin na Gaza, gami da harin baya - bayan nan da aka kai kan matsugunan Yahudawa dake yammacin kogin Jordan.

Wannan dai shi ne hari na farkon da Isra'ila ke kaiwa zirin gaza tun bayan ƙaddamar da tattaunawar sulhu a tsakanin Isra'ila da Falasɗinu a ranar Alhamis da ta gabata.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Zainab Muhammed