1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra´ila ta sake kai farmaki a kan filin jirgin saman Beirut

July 14, 2006
https://p.dw.com/p/BuqY

Duk da suka da take sha daga ko-ina cikin duniya Isra´ila ta ci-gaba da kai hare hare akan sansanonin ´yan Hezbollah da wuraren fararen hula a Libanon. Jiragen saman yakin Isra´ila sun sake kai hari akan filin jirgin saman babban birnin na Libanon sannan kuma sun lalata gadar da ta hada babbar hanya daga Beirut zuwa Damaskus na kasar Syria. Dazu dazu ma Isra´ila ta sake kai farmaki a kan wasu unguwanni dake wajen Beirut, inda hedkwata da kuma tashar radiyon Hizbollah suke. Hukumomi sun ce mutane fiye da 70 daukacinsu fararen hula aka kashe a hare haren da Isra´ila ta shiga kwana na uku tana kaiwa Libanon. Su ma a na su bangaren dakarun Hisbollah sun ci-gaba da harba rokoki cikin arewacin Isra´ila. FM Isra´ila Ehud Olmert ya ce za´a ci-gaba tare da tsananta kai hare haren har sai an kwance damarar kungiyar Hisbollah.