1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra´ila ta sake kai harin roka a birnin Gaza

April 8, 2006
https://p.dw.com/p/Bv2e
Jiragen saman yakin Isra´ila sun sake harba rokoki akan wata mota a birnin Gaza inda suka halaka Falasdinawa ´yan gwagwarmaya biyu. Rundunar sojin Isra´ila ta ce mutanen da aka halaka ´ya´yan kungiyar Al-Aqsa ne wadanda suka harba wani makami mai linzami a cikin Isra´ila. Wannan harin dai ya zo ne kwana daya kacal bayan da wani jirgin saman yakin Isra´ila ya harba makamai masu linzami a kudancin Gaza, inda ya halaka Falasdinawa ´yan gwagwarmaya 5 da kuma wani yaro mai shekaru 7 da haihuwa. Wannan harin dai shi ne mafi muni da Isra´ila ta kai kan Falasdinawa cikin watanni 5.