1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra´ila ta yi barazanar yiwa shugabannin Hamas kisan gilla

May 21, 2007
https://p.dw.com/p/BuKz
Isra´ila ta tsananta hare hare da take kai ta sama akan Zirin Gaza inda a yau ta halaka Falasdinawa 5, 4 daga cikin su ´ya´yam kungiyar Jihadin Islami. Hare haren na yau sun biyo bayan farmakin da Isra´ila ta kai cikin dare ne akan gidan wani dan majalisar dokokin Falasdinu, inda ta halaka mutane 8. Harin dai shine mafi muni tun bayan da Isra´ila ta fara daukar matakan soji da nufin dakile hare haren rokoki daga Gaza zuwa cikin Isra´ila. A kuma halin da ake ciki wani babban ministan Isra´ila ya fid da wani gargadi ga shugabannin kungiyar Hamas. Ministan kula da hanyoyin sadarwa Binyamin Ben-Elizer ya nunar da cewa Isra´ila zata yi farauta tare da halaka duk wani shugaban Hamas dake ba da umarnin harba rokoki cikin Isra´ila. Da farko ministan tsaron cikin gida Avi Dichter cewa yayi zasu yiwa shugaban Hamas dake gudun hijira Kahled Mashaal kisan gilla da zarar damar yin haka ta samu.