1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra´ila ta yi nadama da harin da ta kai kan´jami´an MDD

July 26, 2006
https://p.dw.com/p/Bup6

FM Isra´ila Ehud Olmert ya nuna bakin cikinsa game da mutuwar jami´an sa ido hudu na MDD a wani hari da jiragen saman yakin Isra´ila suka kai a kudancin Libanon. Olmert ya kuma nuna kaduwarsa ga kalaman da babban sakataren MDD Kofi Annan yayi cewa an kai harin ne da gangan. FM ya ce ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike akan wannan lamari da Isra´ila ta bayyana shi da cewa hadari ne. Shi ma kakakin ma´aikatar harkokin wajen Isra´ila Mark Regev ya ce Isra´ila ba zata taba auna makamanta akan jami´an MDD da gangan ba. Da farko dai sakataren MDD Kofi Annan ya bukaci Isra´ila ta gudanar da bincike akan abin da ya kira kai farmaki da gangan akan sansanin MDD a kauyen Khiam a jiya talata. Kasar Sin ta yi Allah wadai da harin wanda a ciki aka halaka dan kasarta daya. Sauran mutum ukun kuwa ´yan kasashen Finland da Austria da kuma Kanada ne.