1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Israila tace a shirye take ta dauki matakin soji

June 26, 2006
https://p.dw.com/p/Busb

Firaministan Israila Ehud Olmert yace sojojinsa suna cikin shirin ko ta kwana,biyowa bayan sace wani sojanta da yan kungiyar sa kai na Palasdinu sukayi.

Ministan harkokin wajen Israila Tzipi Livni tace kasar Israila tana da yancin da kuma hallalcin daukar matakin soji a kokarinta na kwato sojanta da Palasdinawa sukayi garkuwa da shi.

Kakakin maaikatar harkokin wajen Israila Mark Reger yace,Livni,ta fadawa taron jakadun kasashen ketare da suyi Allah wadai da sace wannan soja na Israila.

Sojin sa kai na Palasdinawa suka sace Gilad Shalit dan shekaru 20 daga zirin Gaza cikin wani samame da suka kai a wani shingen binciken sojin Israila wanda yayi sanadiyar mutuwar sojoji 2 wasu 4 kuma suka samu rauni.

Mark Reger ya kara baiyana cewa,ministar tace muddin dai dukkan kokari sun faskara,dole ne Israila tayi anfani da karfin soji wajen ganin ta kwato sojan nata.

Kungiyoyin sa kai 3 na palasdinawa sun dauki alhakin sace sojan na Isrila,kamar yadda suka baiyanawa kanfanin dillancin labarai na AFP amma basu mika wasu bukatu ba domin sake shi.