1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Israila tace zata gina sabuwar katanga

March 10, 2006
https://p.dw.com/p/Bv5O

Kasar Israila tace zata tsage bakin iyakarta da yankin yamma da gabar kogin Jordan,idan baa samu ci gaban tataunawa da Palasdinawa ba,hakazalika tace zata gina sabuwar katanga tare da maido da yahudawa yan share wuri zauna zuwa bangarenta.

Mukaddashin firaminista Ehud Olmert cikin wata hira da jaridar kasar a yau jummaa yace,muddin dai Palasdinawa sun nemi hada kai a kasar Iran to kuwa Israila zata sake canza hanyar katangae yankinta.

Olmert ya kuma yi barazanar kashe sabon firaministan Palasdinu,Ismail Haniyeh na kungiyar Hamas idan an same shi da laifin taaddanci.

A jiya alhamis ne kuma Olmert yace kasar Israila ta kudiri aniyar kammala katangarta a 2010,tare da janyewa daga mafi yawa na yamma da gabar kogin Jordan.

Ehud Olmert wanda ke fuskantar zabe a ranar 28 ga wanna wata,yace katanga da ake ginawa yanzu na tun shekaru 3 da suka shige,na tsaro ne,yayainda sabuwar katanga da zaa gina zata zamo iyaka Israila da gabar kogin Jordan.