1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra´ila zata saki Falasdinawa 250 na bangaren Fatah daga kurkuku

June 26, 2007
https://p.dw.com/p/BuHu

FM Isra´ila Ehud Olmert ya ba da sanarwar sakin firsinoni 250 dukkan su ´ya´yan kungiyar Fatah ta shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas. Lokacin da yake magana a karshen taron kolin da aka yi tsakaninshi da shugabannin Larabawa a wurin shakatawa na Sharmul Sheikh na kasar Masar, FM Olmert ya ce wadannan mutane ba su da jini a hannun su to amma dole su yi alkawarin cewa ba zasu yi amfani da tarzoma ba don cimma burinsu na siyasa. Kimanin Falasdinawa dubu 10 ke zaune yanzu haka a gidajen kurkukun Isra´ila. Shugaban Masar Hosni Mubarak ya bayyana taron kolin a matsayin wani ci-gaba ga farfado da shirin samar da zaman lafiyar yankin GTT. Manufar taron dai shi ne tallfawa shugaba Mahmud Abbas dake mulki a Gabar Yammacin Kogin Jordan bayan da Hamas ta karbi ragamar mulki a Zirin Gaza.