1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Italiya ta amince da tura sojin ta izuwa Libanon

September 27, 2006
https://p.dw.com/p/BuiC

Majalisar dokokin kasar Italiya da babbar murya ta amince da tura sojin kasar dubu 2, 500 izuwa kasar Libanon.

Bataliyar sojin dai zata gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya ne a kasar ta Libanon karkashion laimar Mdd.

A cewar rahotanni kusan yan majalisa 500 ne suka amince da wannan mataki, guda 20 kuma suka hau kujerar naki.

Duk da wannan rinjaye dai da aka samu, dole ne sai wannan kuduri ya samu amincewar majalisar dattijai ta kasar kafin fara aiki a aikace.

Kasar dai ta Italiya na a kann gaban gudanar da wannan aiki na kiyaye zaman lafiyar a kasar ta Libanon, wanda ma ake sa ran a watan fabarairarun sabuwar shekara itace zata karbi ragamar tafiyar da ayyukan kiyaye zaman lafiyar a kasar ta Libanon.