1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Izraela ta fara tayar da sabbin gine-gine a yankin Palastinawa

October 21, 2010

Jakadan Majalisar Ɗunkin Duniya ya soki Izraela akan yankin Palastinawa

https://p.dw.com/p/PkSW
Hoto: Shawgy Al-Farra

Jakadan Majalisar Ɗunkin Duniya a yankin gabas ta tsakiya, ya soki Israela dangane da sake fara gina gidajen 'yan kama wuri zauna a gaɓar yamma da kogin Jordan. Kampanin dillancin labarai na AP ya ruwaito yadda Izraelan ta fara gina gidaje 544, bayan tsagaita shi na watannin goma, zuwa ga ƙarewar wa'adin a watan daya gabata. Palastinawan dai sun fassara wannan sabon yunƙuri na Izraela da kokarin hanasu samun 'yantacciyyar ƙasarsu. Sai dai wa Yahudawan kamar Sanja Lauderdale, abun farin ciki ne sake fara gine-ginen bayan dakatarwa na tsawon lokaci.

" Ta ce mu cigaba da tayar da waɗannan gine-gine, domin samarwa Izraela tsaro da cigaban samun nasarar ƙasarmu,domin nan ɓangaren ƙasar Izraela ne".

A sanarwar da ya gabatar  a yau dai, jakadan Majalisar Ɗunkin Duniya Robert Serry, ya bayyana gine-ginen Izraelan da kasancewa hararantattu domin sun saɓawa dokokin ƙasa da ƙasa, tare da kawo cikas a kokarin da ake yi na warware rikicin da yankin gabas ta tsakiyan ke fama dashi.

Mawallafiyya: Zainab Mohammed Abubakar

Edita: Ahmad Tijani Lawal