1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jadawalin sunayen 'yan tarzoma

Zainab MohammedJanuary 24, 2008

Wasu 'yan majalisar turai masu sassaucin ra'ayi sunyi adawa da tsauraran matakai kan sunayen waɗanda ake zargi da tarzoma

https://p.dw.com/p/CxG4
Tarzoma a turaiHoto: AP

Majalisar tarayyar turai ta gabatarwa da Majalisar Ɗunkin Duniya da ƙungiyar gamayyar turai jerin sunayen ƙungiyoyi da mutane, domin sanyasu cikin jadawalin waɗanda ake zargi da ayyukan ta'addanci.
A Rahotan da Dick Marty ya rubuta na nuna adawa da wannan batu yayi nuni dacewar, tun bayan harin 11 ga watan Satumban 2001 hukumomin guda biyu suka kirkiro wannan jadawalin,wanda ke kunshe da sunayen mutane da ƙungiyoyin da ake zargi da ayyukan tarzoma a sassa daban daban na duniya. Akwai kimanin ƙungiyoyin musulmi sama da 100 da kuma wasu mutane sama da 350 dake jerin wadanda ake zargi da laifuffukan ayyuka dake da nasaba da ta'addanci. "Dick Marty yace muna da rubutaccen takarda dake ɗauke da waɗannan mutane,waɗanda aka rubuta cikin shekaru 6 da suka gabata.Kuma dukkannin waɗanda sunayen da ke cikin jerin an mayar dasu saniyar ware,kana basu da sukunin yawo cikin kasashen ,kuma duk kaddarorin da suka mallaka an rufe su" Kasancewar a yanzu za a sanya idanu a hukumance dangane da jerin waɗannan sunayen da kuma kula da harkokin waɗannan mutane da ƙungiyoyi dai ,ya zame babban matsala a ɓangaren kwarraru ta fannin kare hakkokin jama'a. Dick Marty dake zama Ɗan majalisar turai mai sassaucin ra'ayi wanda kuma sananne ta fannin fafutukar kare hakkin hakkin jama'a,ya rubuta wannan rahoto nasa ne bayan ziyarar daya kai zuwa gidajen kurkukun Amurka dake yankin gabashin turai,inda ya samo bayanai da shaidu,dangane da ire iren wadannan mutane da akanyiwa zargi. Itama 'Yar majalisa Leutheusser-Schnarreberger nada da ra'ayin cewar tsarin jadawalin sunayen 'yan tarzoman ya saɓawa dokar rayuwar bil'adama,wanda zai hana shi walwala cikin harkokin rayuwarsa.
Ɗaya daga cikin mutanen da wannan matsala ta ritsa dasu shine wani ɗan kasuwa,ɗan asalin ƙasar Masar,dake da zama a wani yanki na ƙasar Swizaland Youssef Nada Mai shekaru 76,wanda ake zargi da daukar nauyin aikewa da kuɗade na tafiyar da ayyukan taaddanci.Yanzu haka dai Nada na zaune a gida ,bashi da ikon fita ko ina,kuma an dakatar da dukkan kudaden sa dake asusu. "Youssef Nada yace, abun takaici ne ,ina daurin talala a gida tsawon shekaru shida da suka gabata ,bani da ikon fita ,na kasance tamkar wani kaya ne dake ajiye" A rahotan Ɗan majalisa Marty,wannan tsohon Ɗan kasuwa ya shaidar dacewa bashi da wata alaka da kungiyar Al'qaida kamar yadda ake zargi,sai dai ya kasance member ne a kungiyar yan uwa Musulmi ta Masar,watau muslimen Brotherhood.. "Shekaru 60 da suka gabata ni member ne a wannan kungiya ,inji Nada,kuma tsawon sheakaru 20 dana kasance a turai na ke tafiyar da harkokin siyasar ta.Muna adawa da duk wani yunkuri na tarzoma,kuma hakan bawai akidar mu ce kaɗai ba,amma har bisa ga umurnin addinimmu.