1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jagoran soja ya muzanta 'yan Rohingya

Yusuf Bala Nayaya
October 12, 2017

Janar Min Aung Hlaing babban soja a Myanmar ya bayyana 'yan Rohingya a mtsayin "Bengali", sunan da basa so a bayyanasu da shi.

https://p.dw.com/p/2lgbK
Myanmar General Min Aung Hlaing
Janar Min Aung HlaingHoto: picture-alliance/AP Photo/Aung Shine Oo

Jagoran soja a Myanmar ya bayyana cewa Musulmai 'yan kabilar Rohingya ba 'yan asalin Myanmar ba ne, ya bayyana haka ne kuma a lokacin zantawa da jakadan Amirka. sai dai bai yi masa bayani ba dalla-dalla kan zargin sojansa da ake yi na cin zarafin wadannan al'umma marasa rinjaye a kasar. sai dai ya ce kafafan yada labarai na zarce makadi da rawa kan yadda suke zuzuta labarin.

Janar Min Aung Hlaing ya yi rubutu mai tsawon a kan shafinsa na Facebook wanda yake da muradin duniya ta gani inda a nan ne ya yi jawabi kan ganawar tasa da jakadan na Amirka  Scot Marciel. Janar Min Aung Hlaing da ya bayyana 'yan Rohingya da "Bengali", sunan da basa so a bayyanasu da shi.

Ya ce Turawan mulkin mallaka na Birtaniya su ne kanwa uwar gami a rikicin kasar. Kalaman sojan dai da ke da karfin fada a ji a Myanmar sun nuna rashin tausayawa ga al'ummar da sama da mutane dubu 500 na su suka kauracewa jiharsu ta Rakhine  da ke Arewaci.