1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jagoran 'yan adawa ya bayyana kansa shugaban Gabon

Suleiman BabayoSeptember 3, 2016

An fara samun zaman lafiya a Gabon bayan tashin hankalin da ya biyo bayan sakamakon zaben shugaban kasa da Shugaba Ali Bongo ya samu karamar nasara kan jagoran 'yan adawa Jean Ping.

https://p.dw.com/p/1JvCD
Gabun Opposition Jean Ping Pressekonferenz
Hoto: Getty Images/AFP/S. Jordan

An fara samun zaman lafiya a birnin Libreville fadar gwamnatin kasar Gabon, sakamakon tashe-tashen hankula da suka biyo bayan ayyana Shugaba Ali Bango a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa. Mutane biyar sun hallaka yayin da wasu da dama suka samu raunika, lokacin da aka tabbatar jagoran 'yan adawa Jean Ping ya sha kayi a hannun Shugaba Bongo da kuri'un da suka gaza dubu-shida.

A shekara ta 2009 Ali Bango ya dauki madafun ikon kasar ta Gabon da ke yankin tsakiyar Afirka, bayan rasuwar mahaifinsa Omar Bongo wanda ya kwashe shekaru 42 yana mulkin kasar. Jagoran 'yan adawa Jean Ping wanda yake zama tsohon shugaban hukumar Tarayyar Afirka ya zargin gwamnati da tafka magudi, sannan ya nemi kasashen duniya su saka baki. Tuni Ping ya bayyana kansa a matsayin zababben shugaban kasa, yayin wani taron manema labarai.