1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jakadan Amurka a MDD John Bolton ya yi murabus

December 4, 2006
https://p.dw.com/p/BuZ7

Jakadan Amurka a Majalisar dinkin duniya John Bolton ya sauka daga mukamin sa. John Bolton fitaccen dan jari hujja kuma mai tsananin raáyi a Majalisar dinkin duniya ya zamo jakadan Amurka a Majalisar ta dinkin duniya ne a shekarar ta 2005 bayan nadin da shugaba Bush ya yi masa a kan wannan mukamin. Bush ya yi amfani da ikon sa na shugaban kasa wajen nada John Bolton a matsayi duk kuwa da kakkausar adawa da yan Demokrats suka nuna ta kin jinin manufofi da kuma salon yadda Bolton ke tafiyar da alámura. Kasancewar a yanzu jamíyar Demokrats ce ke da rinjaye a majalisun dokokin biyu na wakilai da kuma Dattijai, sakamakon nasarar da suka samu a zaben da ya gudana a watan da ya gabata, akwai yiwuwar cewa ba za su rattaba amincewa da sabunta nadin sa a wannan matsayi ba a karshen waádin watan janairu na shekara ta 2007