1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jakadan tarayyar Turai ya zargi gwamnatin Sudan kan Dafur

September 13, 2006
https://p.dw.com/p/Bujj

Manzon musamman na ƙungiyar tarayyar turai a ƙasar Sudan Pakka Haavisto ya zargi gwamnatin Sudan da yin luguden wuta a kan fararen hula a yankin Dafur. Haavisto ya shaidawa manema labarai a birnin Khartoum a karshen ziyarar kwanaki uku da ya kai yankin cewa, shi da kan sa, ya ga ganewa idanun sa lokacin da wasu jiragen sama samfurin Antonov mallakar gwamnatin Sudan suke shirin kai farmaki a lardin Dafur. Yace ya kuma ga yara ƙanana wasun su, yan shekaru uku da haihuwa waɗanda suka jikata a sakamakon harin bom. Gwamnatin ta Sudan wadda ke yaƙi da yan tawaye a Dafur, ta ki amincewa da ƙudirin Majalisar ɗinkin duniya na tura sojoji kiman in 20,000 na gamaiyar ƙasa da ƙasa ƙarkashin inuwar majalisar ɗinkin duniya domin aikin kiyaye zaman lafiya a yankin na Dafur mai fama da rikici.