1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jakadun ƙetare sun yi Allah wadarai da cin zarafin kafofin yada labarai a ƙasar Kenya

March 3, 2006
https://p.dw.com/p/Bv6E

Jakadu na ƙasa da ƙasa sun bi sahun yan adawar ƙasar Kenya na yin Allah wadai da dirar mikiyar da yan sandan Kenyan suka yiwa kafofin yada labarai a kasar. Wata sanarwa daga ofishin jakadancin Amurka ta baiyana farmakin da cewa ya saba aƙida ta yancin alúma a tsari na dimokradiyya. Yan sandan sun ce sun kai farmakin ne a kan wani gidan jarida a birnin Nairobi tare da wata tashar Talabijin saboda suna haddasa fitina a tsakanin alúma. Yan sandan sun kuma ƙone jaridu da dama da aka wallafa da kuma rufe gidan Talabijin din. Jaridar ta yin kakkausar suka a game da yadda shugaban kasar Kenyan Mwai kibaki ya ke wasarerai da batun cin hanci da rashawa da ya dabaibaye kasar. Gwamnatin a na ta bangaren ta zargi jaridar da buga labarun karya.