1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamaár kasar Uganda na kada ƙuriá a Zaɓen shugaban ƙasa

February 23, 2006
https://p.dw.com/p/Bv76

A yau dubban jamaár ƙasar Uganda suka fita domin kada kuriá a zaɓen shugaban ƙasa inda ake fafatawa tsakanin shugaban kasar mai ci Yoweri Museveni da kuma madugun adawa Kizza Besigye. Wannan dai shi ne ƙaro na farko a tsawon shekaru 25 da ƙasar ke gudanar da zaɓe bisa tafarkin jamíyu da dama. Yoweri Museveni wanda ya shafe shekaru 20 yana shugabancin ƙasar Uganda na neman goyon bayan alúmar ƙasar domin sake yin tazarce. An tsaurar matakan tsaro domin tabbatar da cikakkiyar kariya ga jamaá a daukacin cibiyoyin zaɓe 20,000 a fadin ƙasar. Kimanin mutane miliyan 10.4 ne ake sa ran zasu fita domin kada kuriá.