1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

James Ibori ya koma Najeriya daga Birtaniya

February 4, 2017

Bayan da ya shafe shekaru hudu a gidan yari bisa dalilai na safarar kudaden haramun, tsohon gwamnan Delta na Najeriya ya koma kasarsa a wannan rana ta Asabar.

https://p.dw.com/p/2WzGU
Wahlen in Nigeria Wahlplakat
Hoto: AP

Daya daga cikin jiga-jigan 'yan siyasar Najeriya kuma tsohon gwamman jihar Delta James Ibori wanda ya yi zaman gidan kaso a Birtaniya bayan samunsa da laifin safarar kudaden haramun ya koma gida Najeriya. Daya daga cikin mukarrabansa Ighoyota Amori ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa Ibori ya sauka Abuja a yau Asabar da safe. Ibori ya yi gwamnan jihar Delta a tsakanin shekarun 1999 zuwa 2007.

An daureshi a shekarar 2012 kan almundahana da dukiyar kasa da suka kai Fam Biliyan 50. A shekarar 2010 ya tsere zuwa Dubai kafin daga bisani hukumomin Birtaniya suka sa aka tasa keyarsa zuwa Birtaniyar inda ya gurfana a gaban kotu. An sakoshi daga gidan yari bayan shafe shekaru hudu daga cikin daurin shekaru 13 da kotu ta yanke masa.