1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamian Iran da Rasha sun fara tattaunawa akan Nukiliya na Iran

February 20, 2006
https://p.dw.com/p/Bv7N

Wata tawagar kasar Iran tuni ta isa kasar Rasha domin tattauna batun nukiliya na kasar da yaki ci yaki cinyewa.

Kasar Rashan dai tayi tayin sarrafa sinadaren uraniyum da Iran take bukata domin makamashi a cikin kasar ta Rasha,batu da Rashan take ganin zai kawo karshen damuwa da kasashen duniya sukeyi game da shirin nukiliya na Iran.

Tattaunawar wannan tawaga kuwa tazo ne a dai dai lokacinda ministan harkokin wajen Iran,Manoucher Mottaki yake ganawa da jamian Kungiyar Taraiyar Turai a birnin Brussels domin tattauna battun kare hakkin bil adama da manufar nukiliya ta Iran .

Kasar ta Iran ta koma sarrafa sinadaren uraniyum a farkon wannan wata,bayan hukumar kula da kare yaduwar makaman nukiliya ta kai ta gaban komitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.