1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jami´an tsaro Jamus sun cafke wani dan Iraqi bisa zargin aikin ta´addanci

October 11, 2006
https://p.dw.com/p/BugF
´Yan sanda a nan Jamus sun kame wani dan Iraqi da ake zargi da yada fafayan bidiyo da na kaset masu dauke da jawaban shugabannin kungiyar al´Qaida ta intanat. Mutumin wanda ya shiga hannun jami´an tsaro a birnin Osnabrück, ana zargin sa da buga jawabai na Osama Bin Laden da Ayman al-Zawahiri da kuma Abu Musab al-Zarqwawi a cikin shekara guda da ta gabata. Masu shigar da kara a birnin Karlsruhe mazaunin kotun kare kundin tsarin mulkin Jamus sun ce ta haka mutumin ya marawa ayyukan ta´addanci baya. Mutumin wanda aka ba da sunansa da Ibrahim R, a yau zai gurfana gaban kotu.