1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jami'an tsaro sun bindige wasu 'yan ta'adda a Diffa

Salissou BoukariJuly 12, 2015

Wasu da ake zaton 'yan kungiyar Boko Haram sun kai hari a wayewar safiyar wannan Lahadin a gidan kason birnin Diffa mai makwabtaka da Tarayyar Najeriya.

https://p.dw.com/p/1FxVC
Nigeria Soldaten in Diffa Aktion gegen Boko Haram
Hoto: Reuters/J. Penney

'Yan bidigar sun hallaka wani kaftin din sojan da ke tsaron gidan kason, tare da jikkata wasu sojojin biyu, amma ba tare da sun saki dan kaso ko daya ba. Jami'an tsaro da suka mayar da martani kan wannan hari sun bindige 'yan ta'addar guda uku kuma suna sanye da jigidar Bam.

Su dai 'yan bindigar da ba'a san adadinsu ba, sun kai harin ne a kafa dauke da gurneti da kuma bindigogi, kuma suna sanye da kayan sojojin na Nijar abun ma da ya basu damar kaiwa har ya gidan kason.Tuni dai jami'an tsaro ke ci gaba da zurfafa bincike, inda aka daukaka Al'kur'ani mai girma domin gano wadanda suke da hannu cikin lamarin.