1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jami'an tsaron yankin yammacin Afirka na ganawa a Senegal

Pinado Abdu WabaNovember 9, 2015

Jami'an na ganawa ne domin gano hanyoyin warware matsalar tsaron da ya addabi yankin, musamman Boko Haram.

https://p.dw.com/p/1H2WZ
Burkina Faso Senegals Präsident Macky Sall
Shugaban kasar Senegal Macky SallHoto: Reuters/J. Penney

Kwararru a fannin tsaro da dama ne ke ganawa a babban birnin kasar Senegal wato Dakar, domin daukan mahimman matakai na kawar da barazanar kungiyar Boko Haram da sauran kungiyoyin masu tada kayar baya a yankin yammacin Afirka.

Jami'ai daga kasashen Mali, da Faransa da Amirka da ma Majalisar Dinkin Duniya ma na halartar wannan taron wanda za su shafe wuni biyu ana yi.

An kaddamar da wannan taron na Senegal din ne sa'oi kadan bayan da mahukuntan kasar suka sanar da cewa sun tsare wasu malamai bisa zarginsu da hada kai da kungiyar Boko Haram.

Da ma dai kungiyar ta Boko Haram ta saba kai hari ne a Najeriya da kasashen da ke kusa da ita, amma da wannan kamen malaman da Senegal ta yi, an sami alamun farko na barazanar kungiyar a kasar wadda mafi yawan al'ummarta musulmi ne masu matsakaicin ra'ayi.

A karshen makon da ya gabata wasu 'yan mata sanya da bama-bamai sun kai harin kunar bakin wake a wata unguwa a Chadi wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.