1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jami'in MƊD ya gana da Suu Kyi

November 27, 2010

Aung San suu Kyi ta ce ta tattauna batutuwa masu muhimmanci tare da manzon sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya(MƊD)

https://p.dw.com/p/QK5h
Aung San Suu Kyi tana yi wa magoya bayanta jawabi bayan sakinta daga daurin talalaHoto: AP

Jagorar fafutukar tabbatar bin tafarkin dimoƙraɗiyya a ƙasar Burma, Aung San Suu Kyi ta gana da wani babban jami'in Majalisar Ɗinkin Duniya a birnin Rangoon da ke ƙasar ta Burma makonni biyu kacal bayan sakinta daga ɗaurin talalar da hukumomin ƙasar suka yi mata. Bayan tattaunawar da ta yi tare da Vijay Nambiar, shugaban ma'aikatan ofishin sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, Ban Ki Moon, Suu Kyi ta shaida wa manema labarai cewar, ganawar ta su ta yi armashi ƙwarai saboda muhimman batutuwa masu ilimantarwar da suka taɓo.

A ranar 13 ga watan Nuwamban nan ne dai hukumomin ƙasar ta Burma suka saki Suu Kyi daga ɗaurin talalar shekaru bakwai da suka yi mata, mako guda kaɗai bayan wani zaɓen da mashahanta suka ke kwatantawa da cewar yaudara ce da ke da nufin wanzar da jagorancin shugabannin mulkin sojin ƙasar.

A yanzun nan da ake batu dai fiye da fursunonin siyasa dubu biyu aka yi amannar cewar suna garƙame a gidajen yarin ƙasar ta Burma. Jam'iyyar National League for Democracy ta Aung San Suu Kyi ta ƙaurace wa zaɓukan ƙasar saboda dokokin da suka yi kama da ƙoƙarin haramta masu adawa da gwamnatin, inda daga baya ma hukumomin ƙasar suka haramta jam'iyyar baki ɗaya.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Halima Balaraba Abbas