1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jami’in Majalisar Ɗinkin Duniya ya gana da shugaban LRA.

November 13, 2006
https://p.dw.com/p/BucM

Babban jami’in Hukumar ba da taimakon agaji ta Majalisar Ɗinkin Duniya, Jan Egeland, ya gana da shugaban ƙungiyar ’yan tawayen LRA ta Uganda, a sansanin ƙungiyar da ke cikin wani ƙundurmin daji a kan iyakar Sudan da Jumhuriyar Dimukraɗiyya ta Kwango. Rahotanni dai sun ce Egeland ya gaza shawo kan shugaban ’yan tawayen, Joseph Kony, da ya sako mata da yara da ƙungiyar ke garkuwa da su. Kotun ƙasa da ƙasa dai na neman Konyn ne ya huskanci shari’a, saboda zargin aikata laifuffuka kan bil’Adama da take yi masa.

A cikin shekaru kusan 20 da aka shafe ana yaƙin basasa tsakanin dakarun gwamnati da ’yan tawaye a arewacin Ugandan dai, dubbanin mutane ne suka rasa rayukansu, sa’annan kusan mutane miliyan biyu kuma ne yaƙin ya tilasa musu ƙaurace wa matsugunansu.