1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyar adawa a Hangari ta yi nasara a zaɓen 'yan majalisar dokoki

April 12, 2010

Jam'iyar FIDESZ ta 'yan adawa a ƙasar Hangari ta samu gagarumar nasara a zaɓen 'yan majalisar dokoki

https://p.dw.com/p/MtVN
Jagoran jam'iyar FDESZ da mai ɗakinsa suna ƙaɗa ƙuri'a a zaɓen jiya lahadiHoto: AP

Jam'iyar 'yan adawa ta masu ra'ayin riƙau a ƙasar Hangari Fidesz ta samu nasara a zagaye na farko na zaɓen 'yan majalisar dokoki da aka gudanar a jiya Lahadi. A sakamakon da aka baiyana na kashi 99 cikin ɗari na ƙuri'un da aka ƙidaya ya nuna cewa jam'iyar 'yan adawar ita ce ke da kashi 52.8 cikin ɗari yayin da jam'iyar dake kan karagar mulki ta 'yan gurguzu wato MSZP take da kashi 19.3, sai jam'iyar masu tsatsauran ra'ayin Jobbik da ke da kashi 16.7 cikin ɗari na ƙuri'un da aka ƙaɗa. A sakamakon da hukumar zaɓen dai ta baiyana jam'iyar ta 'yan adawa wacce ta yi shekaru takwas tana hamaya da gwamnati, a yanzu za ta samu kujeru 206 cikin 386 da ake da su a majalisar dokokin, yayin da jam'iyar 'yan gurguzun da ta sha kaye ke da kujeru 28.

A yanzu dai za a jira a gani ko jam'iyar ta FIDEZ za ta samu rinjaye a majalisar da kashi biyu bisa ukku a zagaye na biyu na zaɓen da za a gudanar a ranar 25 ga watan April, abin da zai iya ba ta damar sake kawo gyara ga kundin tsarin mulkin ƙasar.

Shugaban jam'iyar Viktor Orban tsofon firaministan ƙasar ta Hangari ya baiyana farin cikinsa ga wannan nasara dake zaman ɗaukar fansa, yayin da shugaban ƙasar Laszlo Solyom ya amince da kayen da jam'iyarsa ta sha a zaɓen.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane

Edita : Yahuza Sadissu Madobi