1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamiyar dake mulki ta tasamma lashe zaben Kamaru

July 24, 2007
https://p.dw.com/p/BuFh

Jamiyar shugaba Paul Biya ta RPDC ta lashe zaben majalisar dokoki da kananan hukumomi da aka gudanar a kasar Kamaru da gagarumin rinjaye.Sakamakon bayan fage ya nuna cewa jamiyar dake mulkin ta samu kujeru 152 daga cikin kujeru 180 na majalisar dokoki idan aka kwatanta da kujeru 149 da take da su a tsaohuwar majalisa.Babbar jamiyar adawa ta SDF wadda John Fru ke shugabanta ta kujeru 14 maimakon 22 da take da a tsohuwar majalisa yayinda jamiyar CDU ta Adamou Ndam Njoya ta lashe kujeru 4 sai kuma jamiyar PM mai kujera daya kacal.

Tun farko a jiya litinin jamiyun adawa sunyi korafin an tafka magudi a zaben haka kuma sun lashi takobin kalubalantar sakamakon zaben a gaban kotu yayinda ake ci gaba kirga kuriu.