1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamiyar Demokrat a Amurka ta samu rinjaye a majalisar wakilai

November 8, 2006
https://p.dw.com/p/Buct

Jamiyar demokrats ta samu rinjaye a majalisar wakilai,a zaben da aka gudanar jiya talata.

Nasarar ta jamiyar demokrats ya kawo karshen shekaru 12 da jamiyar republican ke rike da majalisar wakilan.

Jamiyar ta demokrat ta kwato kujeru 15 daga abokiyar hamaiyarta.

Hakazalika a zaben gwamnoni yanzu haka saamakon da aka samu ya zuwa yanzu ya nuna cewa jamiyar demokrat ta lashe zaben a jihohi 26 cikin jihohi 50 .

Kodayake har yanzu ana kusan kunnen doki a majalisar dattijai,inda jamiyar demokrat take bukatar kujeru 6 kafin ta samu rinjaye a majalisar.

Samun nasarar jamiyar demokrat a majalisar wakilai kuwa,yana nufin cewa Nancy Pelosi zata zamo mace ta farko kakakin majalisa kuma mutum na uku a jerin shugabanci a tarihin Amurka.