1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam´iyar Labour ta amince ta janye daga gwamnatin kawance ta Isra´ila

November 20, 2005
https://p.dw.com/p/BvKC

Jam´iyar Labour a Isra´ila ta kada kuri´ar janyewa daga cikin gwamnatin kawance karkashin jagorancin FM Ariel Sharon, don share fagen gudanar da zabe na gaba da wa´adi. Kwamitin jam´iyar ya amince da shawarar da sabon shugaban ta Amir Peretz ya gabatar na janye ministocin sa 8 daga gwamnatin kawance. A gobe litinin ministocin 8 da mataimakan ministoci 3 daga bangaren Labour zasu mika takardun yin murabus. A kuma halin da ake ciki rahotanni sun ce Ariel Sharon ya fara tunani game da makomar sa a fagen siyasa. Ana sa ran cewa FM zai raba gari da jam´iyarsa ta Likud ta masu tsattsauran ra´ayi sannan ya hada kai da tsohon shugaban jam´iyar Labour Shimon Peres duk da janyewar da jam´iyar ta yi daga gwamnatin raba madafun iko. A wani labarin kuma majalisar dokokin Isra´ila ta dage kuri´ar da ta shirya kadawa gobe don sanya ranar gudanar da zabe na gaba da wa´adi, har sai ranar laraba mai zuwa.