1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam´iyar UMP zata lashe zaben ´yan majalisar dokokin Faransa

June 10, 2007
https://p.dw.com/p/BuJM

Makonni 5 bayan zaben shugaban kasa, a yau lahadi masu zabe a Faransa ke kada kuri´a a zagayen farko na zaben ´yan majalisar dokoki. Binciken jin ra´ayin jama´a ya nunar da cewa jam´iyar UMP ta masu ra´ayin mazan jiya karkashin sabon shugaban kasa Nicolas Sarkozy zata lashe zaben. A yau din kuma ake gudanar da zaben ´yan majalisar dokoki a kasar Belgium. Binciken jin ra´ayin masu zabe da aka gudanar ya bawa jam´iyar adawa ta Chiristian Democrats galaba, abin da ke nuni da cewa da wuya FM mai sassaucin ra´ayi Guy Verhofstadt zai yi nasara don samun damar yin tazarce a sabon wa´adin mulki karo na 3.