1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Har yanzu ana samun tsaikon kan sakamakon zaben Myanmar.

Kamaluddeen SaniNovember 10, 2015

Mai magana da yawun Jam'iyyar Adawa a kasar Myanmar dake kudancin Asiya ya soki lamirin hukumar zaben kasar abisa dalilan tsaikon sanar da sakamakon zaben da aka gudanar a ranar lahadin nan.

https://p.dw.com/p/1H2au
Myanmar - Aung San Suu Kyi
Hoto: Getty Images/AFP/Y. Thu

Mai magana da yawun jam'iyyar League Democaratic Party Win Htein ya fadawa manema labarai a yau talatar nan cewar mai yuwane hukumar zaben Myanmar din na wata kunbiya-kunbiya ce ga batun sanar da sakamakon zaben.

Hukumar zaben Myanmar din dai tun ranar lahadin nan ce ta futar da wasu sakamakon zaben a inda sakamakon ke nuni da cewar Jam'iyyar League Democaratic party ce ke kan gaba dake a karkashin jagorancin Au San Syk.

kazalika Win yace yadda hukumar zaben take sakin sakamakon zaben kadan-kadan bai dace ba kamata yayi a bayyana sakamakon baki daya.