1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyyar AfD: "Tsarin Jamus bai dace da Musulunci ba"

Yusuf BalaApril 18, 2016

Jam'iyyar adawar ta AfD ta kasance ta farko da ta bayyana adawa da wani addini tun bayan Hitler a Jamus.

https://p.dw.com/p/1IXpT
Deutschland Beatrix von Storch
Beatrix von Storch daya cikin jiga-jigan jam'iyyar ta AfDHoto: picture alliance/dpa/J. Stratenschulte

Jam'iyyar adawa ta AfD a nan Jamus na ci gaba da shan suka bayan da jagororinta suka bayyana cewa addinin Islama ba zai iya tafiya ba da tsare-tsaren kasar ta Jamus da ma kundin tsarin mulkin kasar.

Jam'iyyar dai ta Alternative for Germany a Turance na yin suka sosai ga gwamnatin shugaba Angela Merkel bisa tsare-tsarenta na karbar baki, inda ma yanzu jam'iyyar take shirin bayyana tsare-tsarenta na kin jinin addinin Islama a taron da za ta yi a wannan wata.

Tuni dai cibiyar mabiya addinin na Islama a nan Jamus karkashin jagorancin Aiman Mazyek ta bayyana cewa wannan jam'iyya ta AfD na rura wutar kin jinin mabiyan na addinin Islama. Mazyek ya fada wa kafar yada labarai ta NDR cewa wannan shi ne karon farko da wata jam'iyya a Jamus ta fito karara tare da nuna kin jinin wani rukunin al'umma saboda addininsu tun bayan gwamnatin Hitler.