1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

JAM'IYYAR ANC NA NUNA ALAMUN LASHE ZABEN AFIRKA TA KUDU

YAHAYA AHMEDApril 15, 2004

Har ila yau dai ana ci gaba da kirga kuri’un da aka ka da, a zaben da aka yi jiya a Afirka Ta Kudu. Farkon kiyasin da muka samu na nuna cewa, jam’iyyar ANC ta shugaba Thabo Mbeki da Nelson Mandela ce ke kan gaba, da kashi 69 cikin dari na kuri’un da aka jefa. Ana ma kyautata zaton cewa, sakamakon karshe da Hukumar zaben kasar za ta bayar, zai bai wa jam’iyyar ta ANC cikakken rinjayi a Majalisar Dokoki.

https://p.dw.com/p/Bvke
Mazauna Soweto, a layin ka da kuri'unsu a zaben Afirka Ta Kudu.
Mazauna Soweto, a layin ka da kuri'unsu a zaben Afirka Ta Kudu.Hoto: AP

Tun kafin a bayyana sakamakon zaben da aka yi jiya a Afirka Ta Kudu a hukumance ma, wasu magoya bayan jam’iyyar ANC ta shugaba Thabo Mbeki da Nelson Mandela, sun fara bikin samun nasara. Kawo yanzu dai, sakamakon da aka samu daga kuri’un da aka kirga na nuna cewa, jami’iyyar ta ANC ta sami kashi 69 cikin dari. Wasu bangarori ma sun kiyasci cewa, jam’iyyar za ta iya samun cikakken rinjayi a duk fadin kasar, abin da zai ba ta damar zartad da dokoki a majalisa ba tare da ta dogara kan abokan hadin gwiwa ba.

Jam’iyyar adawa ta Demokratic Alliance, wadda fararen fata ne suka fi mamaye ta, ita ma a halin yanzu tana da kashi 15 cikin dari. Ita ko jam’iyyar Inkatha ta kabilar Zulu, mai bin ra’ayin `yan kishin kasa, ba ta sami fiye da kashi 5 cikin dari ba, a yadda sakamakon yake a yanzu.

A jiya da safe, kafin ma a bude rumfunan jefa kuri’un, sai da tsohon shugaban kasar, Nelson Mandela, ya yi kira ga duk `yan kasar da su je su ka da kuri’unsu. Bayan ya je ya ka da kuir’a, a karo na 3 a cikin rayuwarsa ne, Nelson Mandela ya cira hannu sama, ya nuna alamun nasara da yatsunsa. Daga bisani ne kuma ya bayyana wa maneman labarai cewa:-

"Hanyar da ta fi inganci gare mu, wajen samun ta cewa a tsarin dimukradiyya, ita ce yin amfani da damar da muke da ita ta shiga zabe, don mu da kanmu mu iya tsai da shawara kan wanda zai yi mana mulki."

Kusan kashi 80 cikin dari na mutane miliyan 21 da suka yi rajistar ka da kuri’u ne ke goyon bayan ra’ayin da Mandela ya bayyana. A wannan karon dai, an sami karin yawan jama’a da suka zabi jam’iyyar ANC da ke mulki, fiye da zabukan 1994 da 1999.

Justin Vandenberg, wani dan kasar mai shekaru 36 da haihuwa, wanda kuma yake da asali daga Jamus, ya shafe fiye da awa 3 a layi, kafin ya iya ka da kuri'arsa a unguwar bakaken fata ta Yeoville a birnin Johannesburg. Ya dai bayyana wa wakiliyarmu, Sandra Petersmann cewa, tun fiye da shekaru dari 3 da suka wuce ne kakanin kakaninsa suka yi kaura zuwa Afirka Ta Kudu. Shi ma, jam’iyyar ANC ya zaba, kamar dai mafi yawan bakaken kasar. A nasa ganin, Afirka Ta Kudu ta sami matukar ci gaba, tun da aka kawo karshen mulkin wariyar al’umma ta Apartheid a kasar. Kazalika kuma yana mai ra’ayin cewa:-

"Mun fi sakewa a nan da Turai, saboda muna da `yanci da yawa nan fiye da Turan. Sabili da haka kuma, muna iya yin ababa da yawa a nan. Da can dai ba a daukan bakaken fata da wani muhimmanci a Afirka Ta Kudu. Amma yanzu ga shi muna Afirka, inda kike mamakin ganin yadda bature ya saki jiki kamar yadda yake so."

Moeletsi Mbeki, wani manaja ne na kafofin sadaswa a Afirka Ta Kudun. Kuma, dan uwan shugaban kasar Thabo Mbeki ne. Babu shakka, shi ma jam’iyyar ANC din ya zaba. Kamar dai wansa, shugaba Thabo Mbeki, Moelesi Mbeki ma ya yi zaman gudun hijira ketare. Dukkansu ba su dawo gida ba, sai bayan sako Nelson Mandela daga kurkuku, a cikin shekarar 1990. Shi ma yana mai ra’ayin cewa, an sami ci gaba a Afirka Ta Kudun, tun farkon zaben da aka taba yi a kasar, shekaru 10 da suka wuce. Amma a nasa ganin, da sauran rina a kaba. Ya dai bayyana cewa:-

"Abin da nake bukata daga gwamnati, shi ne ta kula da talakawan Afirka Ta Kudu. Kamata ya yi ta tsara shirye-shiryen tallafa wa jama’a su fice daga kangin talauci, amma ba ta ci gaba da shirye-shiryen da ke biya wa talakawan wasu daga cikin bukatunsu ba tare da sun iya fita daga da’irar talaucin ba. Abin da na ke sa ran gani, shi ne a kago wani shirin da zai kau da talauci a Afirka Ta Kudu."

kasar ta Afirka Ta Kudu dai na huskantar matsaloli da dama. Fiye da rabin al’umman kasar ne ke fama da talauci har ila yau. Bugu da kari kuma, ba duk ko’ina a kasar ne jama’a ke samun ruwan sha mai tsabta ko kuma wutar lantarki ba. Ga shi kuma dai har ila yau, kusan mutane miliyan 5 ne ke kame da cutar nan ta AIDS a kasar, ba tare da samun wani taimakon kiwon lafiya ba.