1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyyar dake mulki a Ethiopia ta yi iƙirarin yin nasara a zaɓen ƙasar

Umar Saleh SalehMay 25, 2010

Jam'iyyar dake mulki a Ethiopia ta fara shagalin yin nasara tun kafin bayyana cikakken sakamako

https://p.dw.com/p/NW3P
Hoto: AP

Jam'iyyar dake mulki a ƙasar Habasha ta yi ƙiran gudanar da gangamin murnar nasarar manyan zaɓukan ƙasar da aka gudanar a ranar Lahadin data gabata. Sai dai ƙungiyoyin kare haƙƙin jama'a a ƙasar Amirka - ciki harda Human Rigths Watch sun yi zargin cewar an tafka maguɗi a zaɓen. Ɗaruruwan jami'an tsaron ƙasar ne hukumomi suka jibge a wani dandalin dake tsakiyar babban birnin ƙasar Addis Ababa, a dai dai lokacin da magoya bayan jam'iyyar dake mulki ke yin cincirindo domin halartar gangamin. Sai dai kuma ba'a sani ba ko Frime Ministan ƙasar Meles Zenawi zai yi jawabi a wajen taron gangamin.

Nan gaba a yau ne kuma ƙungiyar tarayyar Turai, wadda ta sa ido akan zaɓen ta ce za ta fitar da rahoton ta akan yadda zaɓen ya gudana. Jam'iyyar Ethiopian People's Revolutionary Democratic Front dake kan  mulki, tare da jam'iyyun dake ƙawance da ita ne suka ƙira gangamin, bayan da sakamakon wucin gadi na zaɓen ya nuna cewar, sun yi nasara.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Yahouza Sadisou