1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam´iyyar Fatah da kungiyyar Hamas na kokarin kafa gwamnati

November 12, 2006
https://p.dw.com/p/BucQ

Shugaban yankin Palasdinawa, Mahmud Abbas yace nan da karshen wannan wata da muke ciki, akwai kyakkyawan fatan kafa gwamnatin hadaka ta yankin, a tsakanin jam´iyyar sa ta Fatah da kuma kungiyyar Hamas.

Shugaba Abbas ya shaidar da hakan ne, a jawabin daya gabatar lokacin bukukuwan tunawa da Marigayi malam Yassir Arafat ,a matsayin shekaru biyu cif da rasuwa.

Kokarin kafa gwamnatin hadakar dai a cewar rahotanni, wani yunkuri da yankin yake yi ne, don janyo hankalin kasashen yamma kawo karshen takunkumin tallafin raya kasa da suka aza musu.

Wannan takunkumi da kungiyyar Eu da kuma Amurka suka sakawa yankin na Palasdinawa, abu ne da a yanzu haka ke ci gaba da kawo tsaikon ci gaban ayyukan raya kasa a yankin.

Idan dai an iya tunawa, kasashen na Yamma sun da sakalawa yankin na Palasdinawa takunkumin ne, bayan nasarar da kungiyyar Hamas ta samu ne , a zaben yan majalisar dokokin yankin a watan janairun daya gabata. Kasashen na yamma dai na yiwa kungiyyar ta Hamas kallo ne a mastsayin kungiyya ce ta yan ta´adda.