1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Labour ta yi sabon shugaba a Birtaniya

September 12, 2015

Kasancewar Corbyn jagoran wannan jam'iyya ta Labour na zuwa ne bayan da ya samu kashi 59.5 cikin dari na kuri'un da aka kada.

https://p.dw.com/p/1GVWh
Jeremy Corbyn
Jeremy Corbyn jagoran Labour PartyHoto: picture alliance/empics/D. Lawson

Dan fafutika mai ra'ayin sauyi da ke adawa da shirin tsuke bakin aljihu a Birtaniya Jeremy Corbyn ya zama sabon jagora a jam'iyyar Labour Party da ke zama babbar jam'iyyar adawa a kasar Birtaniya. Kasancewarsa jagoran wannan jam'iyya ta Labour na zuwa ne bayan zaben da aka yi inda ya samu kashi 59.5 cikin dari. Jam'iyyar tasa ta bayyana wannan nasara a ranar Asabar din nan yayin wani taro na musamman da aka tsara.

Mista Corbyn dai ya bayyana bukatarsa ta ganin an samar da makoma ta gari ga Birtaniya. Corbyn ya yi nasara kan Andy Burnham da Yvette Cooper da Liz Kendall.