1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyyar PDP dake mulki a Nijeriya ta kori wasu manyan wakilanta.

April 22, 2010

Jam'iyyar PDP dake shugabancin tarayyar Nijeriya ta sallami manyan mambobin ta 19 bisa yiwa jam'iyya zagon ƙasa.

https://p.dw.com/p/N3w9
Hoto: picture-alliance/dpa

Jam'iyyar PDP dake jagoranci a tarayyar Nijeriya ta dakatar da wakilcin wasu gaggan jam'iyyar su 19 a wannan Alhamis bisa fitowa fili su yi suka ga shugabannin jam'iyyar - lamariin dake ƙara zurfafa saɓanin dake cikin jam'iyyar a yayin da wasu manyan jam'iyyun ƙasar ke sake haɗewa domin tinƙarar zaɓen shugaban ƙasar da za'a yi baɗi - idan Allah ya kaimu. Wata sanarwar da jam'iyyar ta fitar ta bayyana dakatar da mambobin ƙungiyar dake ƙiran karanta da sunan mai fafutukar samar da sauye sauye a cikin jam'iyyar.

Daga cikin jerin sunayen mutanen da jam'iyyar ta dakatar dai harda tsohon shugaban majalisar dattijai a ƙasar da tsoffin ministoci da kuma tsoffin gwamnoni.

Wannan ruɗanin da jam'iyyar ta shiga dai ya zone a ranar da muƙaddashin shugaban ƙasar Dakta Goodluck Jonathan ya sanya hannu akan kasafin kuɗin ƙasar na bana wanda ya tanadi karɓar rancen kuɗi fiye da dalar Amirka miliyan 900 domin gudanar da aikace - aikace ga jama'a. Sai dai tuni wasu 'yan ƙasar suka fara yin suka ga matakin.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Muhammad Nasir Awal.