1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyyar PDP na neman darewa har gida uku

Ubale Musa daga Abuja/ MABMay 23, 2016

Akalla mutane uku na ikirarin shugabantar jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya, wacce jami'an tsaro suke gadin hedikwatarta da ke Abuja babban birnin kasar.

https://p.dw.com/p/1ItCT
Nigeria Regierungspartei PDP
Hoto: DW/K. Gänsler

Jam'iyyar PDP na neman darewa gida uku

Ga masu shagube a harkokin siyasa, sabon shugaban jam'iyyar PDP na zaman Ali Mantu Makarfi, wani sunan da aka harhada daga sunayen shugabanni uku da ke ikirarin jan ragamar harkokinta. Wani rikicin cikin gida a yankin kudu maso Yammacin Najeriya ne dai ya rikide ya kuma kara haukata PDP da ta jima tana zubar da yawu.

Gwagwarmayar neman mallakar ruhin jam'iyyar tsakanin Gwamnan Ekiti Ayodele Fayoshe da kuma Senata daga Ogun Buruji Kashamu ne dai ta kai ga hargitsa lamura tare da rusa shugabancin Ali Sheriff. Abin da ya kai Fayoshen tattaro 'yan uwansa gwamnonin PDP domin jefata cikin sabon rikicin.

Ya zuwa yanzu dai Ahmed Mohammed Makarfin na ikirarin zama shugaban PDP na riko a yayin da Sheriff din ke cewar matakin na Fatakwal ya saba wa dokokin PDP. Ko bayan bangaren na Sheriff da ke ci gaba a cikin ikirarn mallakar jam'iyyar, 'yan sanda na ke gadin hedikwatar PDPda nufin hana barkewar rikici.

Plakat Nigeria Präsidentenwahlkampf
Jami'an tsaro na gadin hedikwatar PDPHoto: DW/U.Haussa

Dattawan PDP sun nada Mantu a matsayin shugaba na rika

Tun a Ranar Lahadi ne dai Sheriff din ya nemi damar amfani da gidan da nufin taron majalisar zartarwar PDP kafin 'yan sanda suce basu san da zamansa ba.

To sai dai kuma an suma dattawan jam'iyyar da suka taru a Abuja a cikin karshen mako suka fitar da Ibrahim Nasir Mantu da Jerry gana domin tafiyar da harkokin PDP. Suka ce basu yarda da zaben na Makarfi ba saboda ba ya cikin dokokin jam'iyyar.

Daga dukkan alamu bangarorin biyu na da jan aiki a gabansu kafin suka kai ga shawo kan gwamnonin mantawa da batun sabon shugabancin na Makarfi. Dokta Umar Ardo da ke zaman jigon jam'iiyar a jihar Adamawa, ya ce shugabancin Makarfi bashi da aibi ga makomar PDP.``