Jam'iyyun kawance a Kwango sun gargadi shugaba Kabila
September 14, 2015A ranar Litinin din nan ce gamayyar jam'iyyun Jamhuriyar Dimokradiyar Kwango suka fada wa shugaban kasar Joseph Kabila cewar take-taken na hannun damansa na nuni da cewar yana kan haramar take tanade- tanaden kundin tsarin mulkin kasar.
Ta cikin wata takarda da ke kunshe da bayanan gargadin da aka rarraba wa manema labarai a kasar ta yi nuni da cewar shugaban gamayyar jam'iyyun da ake kira G7 na bukatar matakan gaggawa na tabbatar da ganin an gudanar da zaben shugabancin kasar da aka tsara a watan Nuwamba na shekara ta 2016.
Sanarwar ta kara da cewar keta kai'dojin kundin tsarin mulkin hatsari ne ga siyasar dimokradiyyar kasar da ta fuskanci yake- yake a shekarun 1996 da 2003 a inda daruruwan rayuka suka salwanta.
Kawo yanzu dai babu wani martani da ya futo daga fadar shugaban kasar kan kalaman na gamayyar jam'iyyun kasar.