1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

JAMUS - AMIRKA

December 6, 2005

Sakatariyar harkokin wajen Amirka, Condoleeza Rice, ta ya da zango na farko a nan Jamus, a ziyarar da za ta kai wa wasu kasashen Turai. Inganta huldodi tsakanin Amirka da nahiyar Turai na cikin muhimman jigogin da za ta tattauna a lokacin ziyararta.

https://p.dw.com/p/Bu3b
Condoleeza Rice
Condoleeza RiceHoto: AP

A ziyarar da take kaiwa a nahiyar Turai, Condoleeza Rice, ta fara ya da zango ne a birnin Berlin. Wannan kuwa, ba abin mamaki ba ne, saboda labaran da suka fito a kwanakin baya, na wani shirin sirri da kungiyar leken asirin Amirka, wato CIA, ke gudanarwa a nahiyar Turai, inda take jigilar fursunonin yaki daga filin jirgin saman Frankfurt zuwa wasu sansanoninta a yankuna daban-daban na nahiyar. To sai dai, jami’an gwamnatin shugaba Bush, sun fi mai da hankalinsu ne kan huldodi tsakanin Jamus da Amirka a halin yanzu. Kamar yadda kakakin ofishin harkokin wajen Amirkan, Sean McCormack, ya bayyanar:-

„Sakatariyar harkokin waje Condoleeza Rice ta dukufa ne wajen ganin cewa an cim ma inganta huldodi tsakanin Amirka da nahiyar Turai. Tuni dai mun fara samun kyakyawan sakamako. Ayyukan hadin gwiwa tsakaninmu da Jamus da sauran kasashen Turai na ci gaba ainun, musamman a yunkurin da muke yi na ganin cewa mun hana Iran mallakar makakaman kare dangi. A kan Afghanistan da Iraqi ma, muna samun kyakyawan sakamako a ayyukan hadin gwiwar da muke gudanarwa a can. Tuni dai mun shawo kan duk wasu bambance-bambancen ra’ayoyin da muka samu a da.“

Shi ma ministan harkokin wajen Jamus, Frank-Walter Steinmeier, ya nanata wannan batun a ziyarar da ya kai a birnin Washington a mamkon da ya gabata. Ya dai bayyana cewa, a cikin yarjejeniyar kafa sabuwar gwamnatin tarayyar Jamus da manyan jam’iyyun kasar suka cim ma, inganta ma’ammala a huldodin dangantaka na ketaren Atlantika, na daya daga cikin muhimman jigajigan manufofin siyar ketare na Jamus. kwararrun masana a harkokin siyasar kasa da kasa ma na ganin cewa, an sami ci gaba a huldodi tsakanin yankunan biyu. Stephen Szabo, wani shaihin malami a jami’ar John-Hopkins da ke birnin Washington, ya bayyana cewa:-

„An sami ci gaba a huskar dangantaka tsakanin yankunan biyu, fiye dai da yadda al’amura suke a lokacin Gerhard Schröder. Amma duk da haka, ba a kai dai ga matsayin da ake a da can ba. Dalilin haka kuwa, shi ne yanzu ba alkibla daya bangarorin biyu ke bi ba. Ko wanne na da inda ya fi ba da muhimmanci wajen kare maslaharsa.“

Tun da aka kawo karshen yakin cacar baka ne dai, aka sami sauyi a manufofin harkokin wajen Amirka. Sa’annan harin ran 11 ga watan Satumba kuma, ya sa Amirka ta fi ba da fiffiko ne ga yaki da ta’addanci. A wannan huskar kuwa, ko da tsohuwar gwamnatin Jamus ma, Amirka ta sami hadin kai.

Kafin dai ta fara ziyararta a nahiyar Turai, Condoleeza Rice, ta bayyana cewa, ta wasu bayanan da kungiyar laken asirin CIA ta bayar, an iya cim ma ceto rayukan mutane da yawa a nahiyar Turai. A wannan huskar ta musayar labarai na sirri dai, masana harkokin siyasar kasa da kasa sun ce, duk bangaroin biyu za su iya samun fa’ida.

Sai dai har ila yau a Amirka, akwai masu gunagunai da Jamus, saboda matsayin da ta dauka a lokacin afka wa Iraqi da yaki. To abin da ake tambaya a nan shi ne, yaya Jamusawa ma ke ganin manufofin Amirkan a halin yanzu ?