1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: An dage tattaunawa kafa gwamnati

Gazali Abdou Tasawa
January 29, 2018

A Jamus tattaunawa da ake tsakanin jam'iyya mai mulki da kuma babbar jam'iyyar adawa ta SPD a kokarin kulla kawancen kafa sabuwar gwamnati ta tsaya cik bayan da bangarorin biyu suka kasa samun fahimtar juna. 

https://p.dw.com/p/2rgN8
Berlin Koalitionsverhandlungen zwischen Union und SPD
Hoto: pictur-alliance/dpa/G. Fischer

A kasar Jamus tattaunawa da ake tsakanin jam'iyya mai mulki da kuma babbar jam'iyyar adawa ta SPD a kokarin kulla kawancen kafa sabuwar gwamnati ta tsaya cik bayan da har a tsakiyar daren jiya bangarorin biyu suka kasa samun fahimtar juna. 

A yanzu dai an dage tattaunawar tare da kafa wani kwamiti da zai fito da shawarwari na warware batutuwan da ke kawo cikas ga tattaunawar bangarorin biyu, shawarwarin da kwamitin zai gabatar a yinin yau. 

Daya daga cikin batutuwan da ke kawo cikas a tattaunawar dai shi ne bukatar da jam'iyyar SPD ta ke da ta ganin an sake nazarin batun hadewar iyalan 'yan gudun hijira masu izinin zaman kasa na dindindin a wuri daya.