1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus da batun 'yan gudun hijira

Lateefa Mustapha Ja'afarAugust 25, 2016

Muhawara ta kaure dangane da kalaman shugabar gwamnatin Jamus kan batun 'yan gudun hijira na "Za mu iya" DW ta ji ra'ayin 'yan kasa.

https://p.dw.com/p/1JpiF
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel
Shugabar gwamnatin Jamus Angela MerkelHoto: Getty Images/Gallup

A shekara ta 2015 yayin da kaashen nahiyar Turai suka tsinci kansu cikin halin kwararar bakin haur da 'yan gudun hijira mafi akasari wadanda ke tserewa rikicin Siriya, Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bude kan iyakokin kasarta ga dubban 'yan gudun hijira tare da yin wasu kalami na "Za mu iya". Sai dai yanzu da Jamsu din ta fuskanci hare-haren ta'addnci guda biyu a wannan shekara ta 2916, wasu Jamusawa sun fara tunani kan batun na Merkel.