1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus da Faransa sun buƙaci tura jami´an tsaron ƙasa da ƙasa a Kirgistan

July 17, 2010

Mutane dubu biyu ne suka rasu a rikicin ƙabilanci wannan shekara a ƙasar Kirgistan

https://p.dw.com/p/OO0n
Kouchner tare da WesterwelleHoto: Marcin Antosiewicz

Jamus da Faransa sun yi kira ga ƙungiyar tabbatar da tsaron ƙasashen Turai da ta tura 'yan sandan tabbatar da zaman lafiya a ƙasar Kirgistan.

A wani taron ministocin ƙasashen Turai da ke gudana a kazakhstan, ministan harakokin wajen Jamus Guido Westerwelle da takwaransa na Faransa Bernad Koucher, sun bayyana fatan samar da 'yan sandan zai taimaka gaya, wajen inganta halin tsaro a ƙasar da tayi fama da tashin hankalin siyasa da ƙabilanci a kwannan nan tsakanin ƙabilar Uzbek da Kyrgiz wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane a ƙalla 2000.

A jiya Juma'a ne dai ƙungiyar samar da tsaron a Turai da gwamnatin wucin gadin Kirgistan suka amince da tura jami'an tsaro  52 har na tsawon wata huɗu kana daga bisani a ƙara yawan su da wasu 50, domin bada shawara akan hanyoyin tabbatar da tsaro a ƙasar.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Yahouza Sadissou Madobi