1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus da Indiya sun tabbatar da aiki tare

May 30, 2017

Shugabwar Gwamnatin Jamus Angela Merkel da ta karbi bakuncin Firaminista Narendra Modi na Indiya ta nuna muhimmanci aiki tare.

https://p.dw.com/p/2drQq
Deutsch-indische Regierungskonsultationen in Berlin | Angela Merkel & Narendra Modi
Hoto: Reuters/H. Hanschke

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi taron manema labarai Firaminista Narendra Modi na kasar Indiya, wanda yake ziyara a kasar ta Jamus, inda kasashen biyu suka yi alkawarin aiki tare ta fannin tabbatar da ci gaba a kasashen duniya.

Tattaunawa tsakanin shugabannin biyu ta mayar da hankali kan fannonin hadin kai a bangaren fasaha, da makamashi, gami da yaki da ta'addanci. Kana kasashen na Jamus da Indiya sun saka hannu kan yarjeniyoyiy da suka kulla lokacin ziyarar ta firaministan Indiya a birnin Berlin.

Sannan Jamus ta nuna jin dadi kan yadda Indiya ta rungumi bangaren makamashi da ake sabunta mai amfani da hasken rana, wanda Jamus ta kware a kai. Jamus ta kasance babbar kawa ga Indiya cikin kasashen Tarayyar Turai, abin da ya saka wannan ziyara ta Firaminista Narendra Modi take da muhimmanci a kasar ta Jamus.