1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus da Nijar za su karfafa hadin kan yaki da tarzoma

Abdoulaye Mamane Amadou MNA
July 31, 2017

Ministar tsaron Jamus Ursula von der Leyen da ta kai ziyara a Yamai ta tattauna da hukumomin Nijar kan yaki da ta'addanci a yankin Sahel.

https://p.dw.com/p/2hSGK
Afrika Kanzlerin Merkel besucht Niger
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou a wata ziyara da ta kai Yamai a watan Oktoban 2016Hoto: Getty Images/AFP/B. Hama

Duk da yunkurin kasashen Tarayyar Turai na fatan ganin an murkushe aiyukan kungiyoyin 'yan ta'adda masu haifar da mummunar barazana ga tsaro musamman ma a kasashen G5 Sahel, har yanzu wankin hula na bukatar ya kai dare, inda matsalolin kungiyoyin 'yan ta'adda ke neman su gagari kundila.

Ursula von der Leyen ita ce ministar tsaron kasar Jamus da ta kai ziyara birnin Yamai a wannan Litinin, ta kuma sheda wa DW batutuwan da suka daddage tare da shugaban kasa.

"Na zo Nijar ne don tattaunawa da hukumomin kolin kasar kan batutuwan tsaro da ma batutuwan tallfa wa Nijar da sauran kasashen G5 Sahel. Na kuma tattauna da shugaban kasa kan maganar kafa rundunar kasashen G5 Sahel tare da duba iya adadin tallafin da kasar Jamus za ta kawo wa wannan runduna."

Mali Deutschland Ursula von der Leyen besucht Bundeswehr Soldaten in Gao
Ministar tsaron Jamus Ursula von der Leyen a ziyarar da ta kai wa sojojin Jamus a yankin SahelHoto: Reuters/M.Kappeler

Tawagar ministar ta kuma kai ziyara a wasu muhimman wurare musamman ma sansanin askarawan kasar Jamus da ke aikin tabbatar da tsaro a Mali da ke babban birnin Yamai tare da ganawa da ministocin tsaro da na cikin gida duk dai da zummar tallafa wa kasar yin fito na fito da aiyukan ta'addanci.

Burin Nijar ga Jamus da sauran kasashen Turai

Malam Kalla Muntari shi ne ministan tsaron Nijar da ya ce sun tattauna kan batutuwa daban-daban da ke tsakaninsu da Jamus da burinsu ga kasashen Turai.

"Babban buri shi ne taimako na ci-gaban kasarmu da taimako na aikin wanzar da zaman lafiya."

Kasashen dai na G5 Sahel da ministar take ziyarta na da bukatar makudan kudade fiye da Euro miliyan 450 don girka wata kasaitacciyar runduna da za ta tsaya da kafafunta don yi wa kanta kiyamin laili wajen yaki da masu dauke da makamai, tsarin da kasar Jamus ta ce za ta taimakawa a yayin da wasu kasashe har ma da Majalisar Dinkin Duniya suka nuna dari-dari wajen inganta rundunar.