1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Hadin gwiwa

YAHAYA AHMEDNovember 14, 2005

A karshen makon da ya gabata ne shugabannin jam'iyyun SPD da na CDU/CSU suka ba da sanarwar cim ma yarjejeniyar kafa gwamnatin hadin gwiwa tsakaninsu.

https://p.dw.com/p/Bu4C
Kundin yarjejeniyar
Kundin yarjejeniyarHoto: dpa

A taron maneman labaran da shugabannin manyan jam’iyyun biyu na Jamus suka kira, don gabatad da yarjejeniyar kafa gwamnatin hadin gwiwar da suka cim ma a karshen mako, Angela Merkel da Franz Müntefering sun nuna farin cikinsu ga sakamakon da doguwar tattaunawarsu ta haifar. Dukkansu dai sun bayyana cewa, za a huskanci wani mawuyacin hali na tattalin arziki nan gaba, kafin al’amura su fara kyautatuwa. Yarjejeniyar da suka cim ma dai, ta kunshi shafi 100 ne a rubuce, wadanda ke bayyana duk irin matakan da sabuwar gwamnatin hadin gwiwar za ta dauka da nufin shawo kan komadar tattalin arzikin da ake huskanta.

Da farko dai, matakan za su fara aiki ne, shekara daya bayan kafa gwamnatin, wato a cikin shekara ta 2007 ke nan. A cikin wannan shekara dayan dai, abokan hulda a gwamnatin ta tarayya na kyautata zaton cewa, za a sami farfadowar tattalin arziki, abin da zai ba da damar aiwatad da matakan. A cikinsu kuwa har da daga yawan haraji kann kayayyakin masarufin da ake biya, wanda aka fi sani da suna VAT a takaice, daga kashi 16 zuwa kashi 19 cikin cikin dari. Kazalika kuma, za a tsawaita lokacin gwajin ma’aikata daga wata shida zuwa shekaru biyu. Wato a duk tsawon wannan lokacin, za a iya sallamar ma’aikaci daga gun aikinsa, ba tare da yana da wata kariya a huskar shari’a ba. Duk bangarorin biyu dai sun yarje kan wannan matakin, da kuma wasu matakan rage gibin kasafin kudin da za a dauka.

A shekara mai zuwa ne kuma, za a soke tallafin da ake bai wa masu gidajen kansu. Kazalika kuma za a rage kudin sufuri da ake bai wa ma’aikata, masu tafiya mai nisa daga mazuninsu zuwa wuraren aikinsu. Kwaskwarimar da za a yi wa tsarin kafofin tarayya kuma na cikin muhimman ababan da aka cim ma a yarjejeniyar.

Jam’iyyun SPD da na CDU/CSU dai, sun yi duk iyakacin kokarinsu wajen kaucewa daga duk wasu rikice-rikice da kuma bambancin ra’ayoyin da za su iya janyo sabani tsakaninsu a lokacin tattaunawar. Sai dai duk da haka, ba su cim ma daidaito a kan wasu muhimman batutuwan ba. A lal misali na kwaskwarimar da za yi wa tsarin kiwon lafiya ko kuma soke duk wasu shirye-shiryen gina tashoshin makamashin nukiliya. To sai gwamnatin ta fara aikinta ne dai, za a ga yadda bangarorin biyu, za su iya kauce wa barkewar rikici a kan wadannan batutuwan.

A takaice dai, za a iya cewa, yarjejeniyar da aka cim ma ta kafa wannan gwamnatin hadin gwiwar ta tarayyar Jamus, ta bambanta ainun da wasu da aka cim ma a da, ko kuma da irin sauyin da aka samu a shekarar 1982. Abin da masharhanta ke gani yanzu dai shi ne, watakila, a wannan karon duk manyan jam’iyyun biyu, wato SPD da CDU/CSU, za su ajiye batutuwan da suke ta jayayya a kai saboda dalilan siyasa da bambancin ra’ayoyi a gefe, don su iya dukufad da lokacinsu wajen daukan matakan farfado da tattalin arzikin Jamus.

A lokacin yakin neman zabe dai, duk jam’iyyun biyu sun sha sukar juna da da shafa wa sunan daya jam’iyyar da suke adawa da ita kashin kaza.

To a yanzu, bayan zaben, inda a karshe dai Angela Merkel ce ta kasance, wadda za ta shugabanci sabuwar gwamnati, kuma tamkar mace, wadda ta taba rike wannan mukamin a karo na farko a tarihin Jamus, kamata ya yi duk jami’an gwamnatin su yi hobbasa, su zage dantse su ba ta duk irin gudummuwar da take bukata, don ta iya aiwatad da shirye-shiryen da ta sanya a gaba na ceto tattalin arzikin Jamus daga kara tabarbarewa. Idan matakan gwamnatin da za ta shugabancin suka ci nasara, to duk Jamusawa ne za su ci moriyar fa’idar da za su janyo.