1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta aike da jiragen yaki zuwa Siriya

Zainab Mohammed AbubakarDecember 10, 2015

A wani mataki na cikanta alkawarin da ta daukarwa makwabciyarta Faransa bayan harin 13 ga watan Nuwamba, Jamus ta fara aikewa da dakarunta zuwa Siriya.

https://p.dw.com/p/1HLLD
Deutschland Syrien-Einsatz Tornado Aufklärungsflugzeug
Hoto: Getty Images/S. Gallup

Jamus ta aike da rukunin farko na jiragen yaki samfurin Tonado guda biyu da na jigilar jami'an soji kirar A400M, zuwa sansanin dakarun kawancen tsaro na NATO da ke kasar Turkiyya. Kazalika ayarin jami'an soji 40 maza da mata na kan hanyarsu zuwa wannan yanki , acewar rundunar tsaron Jamus ta Budeswehr. Tarayyar Jamus dai na muradin aikewa da jaiaragen yaki sanfurin Tonado guda shida. Ana muradin fara amfani da wadannan jiragen a kasar Siriya a watan Janairu, wanda ke nufin cikanta alkawarin da Jamus ta daukarwa Faransa na taimaka mata wajen yaki da kungiyar IS. Bisa ga yarjejeniyar da aka cimma a majalisar dokokin kasar ta Bundestag dai, Jamus ba zata shiga yakin da ake yi da IS a Siriya da Iraki kai tsaye ba.