1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta amince da shirin samun mafaka

Suleiman BabayoOctober 16, 2015

An amince da sabon shirin tsaurara neman mafaka a Jamus da suka hada da hana wadanda suka fito daga wuraren da akwai zaman lafiya.

https://p.dw.com/p/1GpMf
Deutschland Bundesrat Abstimmung Asylrecht
Hoto: picture-alliance/dpa/K. Nietfeld

Majalisar dokokin Jamus ta Bundestag ta amince da shirin shugabar gwamnati Angela Merkel kan tsaurara dokokin samun mafaka a kasar, da suka hada da mayar da 'yan kasashen yankin Balkan gida, saboda ba sa cikin kasashe da ke bukatar kariya. Kasashen sun hada da Albaniya, da Kosovo da kuma Montenegro. Sannan za a hanzarta kula da tarkardun wadanda suka fito daga kasashen da ake samun rikice-rikice kamar Siriya.

Tuni babbar majalisar dokoki, ta Bundesrat, wadda ta kunshi gwamnoni jihohi 16 na kasar, ta amince da ayar dokar bayan karamar majalisa ta Bundestag ta amince a wannan Alhamis da ta gabata. Wani hasashen gwamnati ya nuna yuwuwar fiye da masu neman mafaka 800,000 za su saka kafa a kasar ta Jamus, wadda ke daya daga cikin manyan kasashen duniya masu karfin tattalin arziki.