1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta amince da wani gagarumin shirin farfado da tattalin arzikin kasar

January 10, 2006
https://p.dw.com/p/BvCv

Gwamnatin tarayyar Jamus ta amince da wani shiri da zai ci kudi Euro miliyan dubu 25 don farfado da tattalin arzikin kasar. Ministoci sun ce wadannan kudade zasu taimaka a rage yawan marasa aikin yi, bunkasa tattalin arziki tare da yin rangwamin haraji ga masu zuba jari a cikin kasar. A yau rana ta karshe a taron yini biyu da suke yi a garin Genshagen, membobin majalisar ministocin shugabar gwamnati Angela Merkel zasu mayar da hankali akan kasafin kudin gwamnatin tarayya na shekara ta 2006 da shekara ta 2007. Ana sa rai mahalarta taron zasu kuma tattauna akan kirkiro da tsarin karancin albashi, sauye-sauye a fannin kiwon lafiya sai kuma manufofin makamashi na gwamnatin tarayya.