1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta capke yan ta´ada 3

September 5, 2007
https://p.dw.com/p/BuCH

Tsakanin daren jiya, zuwa sahiyar yau,Jami´an tsaro a nan ƙasar Jamus, sun capke wasu mutane 3, da su ke zargi da shirya hare-haren ta´adanci.

A yayin da ya ke bada wannan labari, ministan tsaron Jamus, Franz Josef Jung, ya ce ƙasar na fuskantar wata barazana daga yan ta´ada, to amma gwamnati ta ɗauki matakai ƙwaƙwara na riga kafi ,da kuma na murƙushe yan ta´ada a duk inda su ke a fadin Jamus.

Saidai ministan bai bada cikkaken bayyani ba, a game da wannan shiri na kai hari.

Gabanin sa, wata tashar gidan redio ta ce, yan ta´adan sun ƙudurci abkawa filin saukar jiragen sama na birnin Frankfort, ɗaya daga wanda su ka fi girma a duk nahiyar turai, da kuma sassannin sojojin Amurika da ke Ramstein a yammacin Jamus.

Rediyon ta ƙara da cewar, 2 daga yan ta´dan jamusawa ne, sai kuma na ukun su, ƙan ƙasar Pakistan.